China na aikata kisan kare dangi kan 'yan kabilar Uighur musulmi - Rahoto

Yankin Xinjiang da ake azzabatar da 'yan kabilar Uighur
Yankin Xinjiang da ake azzabatar da 'yan kabilar Uighur GREG BAKER AFP/File

Wani binciken masana yace kasar China na aikata kisan kare dangi kan 'Yan kabilar Uighur Musulmi ganin yadda hukumomin kasar ke azabtar da su ta hanyoyin da Majalisar Dinkin Duniya ta haramta.

Talla

Rahotan da Cibiyar Binciken Washington ta gabatar ya bayyana irin nauyin da China zata dauka kan abinda ke faruwa a kasar ta sakamakon bincike mai zaman kan sa da aka gudanar a kan abinda take aikatawa a arewa maso yammacin Xinjiang.

Masu kare hakkin Bil Adama sun bayyana Yankin Xinjiang a matsayin wanda ya zama dandalin kisan gilla da aka tsare akalla mutane miliyan guda, wanda China ke cewa tana koya musu sana’oi ne.

Rahotan binciken yace 'Yan kabilar Uighur na fama da radadin wannan matsalar a jikin su da kuma kwakwalwar su saboda azabtarwa da cin zarafi da fyade da kuma yadda ake kunyata su a idon jama’a a sansanin da ake tsare su.

Gwamnatin Amurka ta Donald Trump da ta bar karagar mulki ta bayyana cewar China na aikata kisan kare dangi kan 'Yan kabilar Uighur wadanda akasarin su Musulmai ne.

'Yan Majalisun Canada sun kada kuri’a a watan jiya domin bayyana yadda China ke azabtar da 'Yan kabilar Uighur a matsayin kisan kare dangi, yayin da 'Yan majalisun kasar suka bukaci Firaminista Justin Trudeau da ya amince da haka a hukumance.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.