Brazil-Silva

Lula da Silva na Brazil ya koma siyasa bayan wanke shi daga zargin rashawa

Tsohon shugaban kasar Brazil Lula da Silva bayan wanke shi daga zargin rashawa.
Tsohon shugaban kasar Brazil Lula da Silva bayan wanke shi daga zargin rashawa. REUTERS - AMANDA PEROBELLI

Tsohon shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya sake komawa fagen Siyasa, inda ya caccaki shugaba mai ci Jair Bolsonaro kan yadda ya gaza dakile annobar corona da ta lakume rayukan ‘yan kasar ta Brazil fiye da dubu 200.

Talla

Lula da ya shugabanci Brazil daga 2003 zuwa 2010 ya sake bayyana a matsayin wanda ke kan gaba tsakanin wadanda za su kalubalanci shugaba Bolsonaro a zaben badi ne, bayan da kotun kolin kasar ta wanke shi daga zargin rashawa tare da soke hukuncin daurin gwamman shekarun da aka yanke masa a baya.

Yayin gabatar da jawabinsa na farko bayan hukuncin kotun kolin, Lula da Silva mai shekaru 75, ya yi tir da gazawar shugaba Bolsonaro kan tattalin arziki da kuma sakaci kan annobar corona da kawo yanzu ta kashe mutane fiye da 266 a kasar ta Brazil, adadi mafi yawa a Duniya bayan na Amurka.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama'a a baya bayan nan, ta nuna Lula zai iya lashe zaben Brazil da ke tafe a 2022, la’akari da karbuwarsa ga al’ummar kasar, duba da rawar da ya taka wajen bunkasa tattalin arziki a lokacin shugabancinsa.

Lula da Silva da har yanzu bai ce komai ba dangane da tsayawa takara a zaben da ke tafe, ya bayyana hukucin daurin shekaru 26 kan laifukan rashawa da aka taba yanke masa, a matsayin karya mafi muni a fannin shari’a cikin shekaru 500.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.