Amurka-Biden

Majalisar Amurka ta amince da kunshin rage radadin coronavirus

Kunshin rage radadin Coronavirus din shi ne mafi girma da zai shafi miliyoyin al'ummar Amurkan.
Kunshin rage radadin Coronavirus din shi ne mafi girma da zai shafi miliyoyin al'ummar Amurkan. AFP/File

Majalisar wakilan Amurka ta amince da kunshin shirin tallafawa Amurkawa don rage musu radadin Coronavirus da shugaba Joe Biden ya gabatar mata, amincewar da ke matsayin babbar nasara ga shugaban da ke fatan kudaden su cire tarin al’ummar kasar da kamfanonin daga matsin tattalin arzikin ad Coronavirus ta haifar musu.

Talla

Kunshin kudin tallafin da yawansa ya kai dala tiriliyan 1 da Biliyan 900 karkashin shirin tayar da komadar sassan kasuwanci da daidaikun mutanen wadanda Coronavirus ta yiwa illa, kimanin tiriliyan 1 da biliyan 400 zai tafi bangaren daidakun Amurkawa ya tsallake majalisar majalisar ne ba tare da goyon bayan ko da kuri’a daya daga bangaren ‘yan Republican ba.

Shirin tallafawa Amurkan zai zama nasara mafi girma da Biden ya samu haka zalika shiri mafi girma tun bayan hawansa Mulki da zai amfani daidaikun al’ummar kasar musamman masu karamin karfi da kananan masana’antu.

Sai dai Jam’iyyar Republican wadda ta ki kada kuri’a ga kudirin na Biden tya zargi shugaban da saba alkawarin da ya daukarwa al’ummar kasar yayin bikin rantsar da shi a watan janairu bisa kafa hujja da yadda kunshin tallafin zai yi tasiri wajen raba kan al’ummar kasar da kuma nuna bambanci.

Tuni dai fadar White House ta fitar da sanarwa game da nasarar ta Biden gaban Majalisa kan kudirin, yayinda ta ce a juma’a mai zuwa shugaban zai sanya hannu tare da mayar da kudirin doka, kwanaki kalilan gabanin karewar wa’adin shirin tallafawa marasa aikin yin a kasar da ke amfanar da miliyoyin al’ummar kasar.

Daga cikin kasafin da shirin ya kunsa akwai, rabawa gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi dala biliyan 350, dala biliyan 130 ga makarantu, sai kuma dala biliyan 49 da za a yi amfani da su wajen fadada Shirin yiwa mutane gwajin Korona, yayin da aka ware dala biliyan 14 don aikin raba alluran rigakafin cutar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.