Birtaniya

'Yan biyun da ake haifa a fadin Duniya sun karu -Oxford

wani asibiti da aka jibge yan biyu
wani asibiti da aka jibge yan biyu AFP - SERGEI SUPINSKY

Wani bincike da jami’ar Oxford ta kasar Birtaniya ta gudanar, ya gano cewa yawan ‘yan biyun da ake haifa a fadin Duniya ya karu fiye da yadda ake haifa a baya.

Talla

Rahoton binciken, ya nuna cewa ana haifar ‘yan biyu miliyan 1 da dubu dari 6 ninki uku kenan idan aka kwatanta da shekaru 30 da suka gabata.

A cewar shugaban tawagar masu gudanar da binciken Christian Monden ya ce yawan yadda ake haifar tagwaye ya karu matuka.

Sakamakon binciken ya kara da cewa, mata kan ziyarci likitoci don ayi musu dashen ‘yan biyun, saboda ci gaban fasaha da aka samu a Duniya, wanda shine musababin karuwar haihuwar ‘yan biyun a Duniya.

Binciken ya kuma gano cewa Amurka da tarayyar Turai, sune ke gaba wajen kara yawaitar haifar ‘yan biyun kasancewar nan matan suka fi zuwa don ayiu musu dashen ‘yan biyun.

An dai gudanar da binciken a kasashe 165 a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015.

Sakamakon binciken ya kara da cewa adadin ‘yan biyun da ake haifa a arewacin Amurka ya zarta na ko in a fadin duniya da kaso 71 sai na yankin asiya da ke biye masa baya da kaso 32.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.