Corona-AstraZeneca

WHO ta bukaci kasashe su ci gaba da amfani da allurar AstraZeneca

Alluran rigakafin AstraZeneca da yanzu haka wasu kasashen Turai suka fara daina amfani da shi biyo bayan yadda ya ke haddasa daskarewar jini ga wasu da aka yiwa.
Alluran rigakafin AstraZeneca da yanzu haka wasu kasashen Turai suka fara daina amfani da shi biyo bayan yadda ya ke haddasa daskarewar jini ga wasu da aka yiwa. REUTERS - DADO RUVIC

Yayin da manyan  kasashen duniya cikin su harda Jamus da Faransa da Italia suka dakatar da amfani da maganin rigakafin cutar korona na AstraZeneca saboda rahotannin illar da aka ce yanayi, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bukaci ci gaba da amfani da allurar.

Talla

Babbar jami’ar kimiyar hukumar Soumya Swaminathan ta ce basa bukatar mutane su shiga rudani, saboda haka su na bukatar ci gaba da karbar allurar rigakafin na AstraZeneca.

Rahotanni daga wasu kasashen Turai sun nuna cewar ana danganta maganin da daskarewar jinin da ake samu a jikin wadanda suka karbi allurar.

Wannan ya jefa fargaba tsakanin mutane da dama, abinda ya sa wasu kasashe su dakatar da amfani da maganin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.