Amurka-Rasha

Biden na Amurka ya bayyana Putin na Rasha a matsayin rikakken makashi

Shugaba Joe Biden na Amurka da takwaransa Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Joe Biden na Amurka da takwaransa Vladimir Putin na Rasha. AFP - ERIC BARADAT,PAVEL GOLOVKIN

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya amince 100 bisa 100 da rahoton da ke bayyana takwaransa shugaban Rasha Vladimir Putin a matsayin Makashi.

Talla

Yayin zantawa da kafar yada labarai ta ABC News a yau Laraba, Biden ya sha alwashin daukar matakin ramuwar gayya kan Putin sakamakon kokarin da ya yi na haifarwa da takararsa cikas a zaben shugabancin Amurka da ya gudana a shekarar bara ta 2020, kamar yadda binciken jami’an sirri na kasar ya tabbatar.

A lokacin da aka nemi tsokacin shugaban na Amurka kan zargin da ake yi wa takwaransa na Rasha wajen yiwa ‘yan adawa mugunta da kuma kisa, sai ya kada baki ya ce ba shakka haka abin ya ke Putin mugu ne.

Sai dai Biden bai fayyace ko zai yi wa Putin raddi ne kan kokarin yin katsalandan a zaben shugabancin kasar ba, ko kuma kan wasu batutuwa da Amurka ke adawa da su, da suka hada da shayar da jagoran ‘yan adawar Rasha Alaxei Navalny guba, da kuma cigaba da garkame shi a gidan yari.

Kalaman na Biden dai sun yi hannun riga da matsayar  tsohon shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya rika kaucewa aibata shugaban na Rasha.

Tuni dai gwamnatin Rasha ta mai da martani kakkausa kan kalaman shugaba Joe Biden da ta yi tir da su, yayin da shi kuma kakakin majalisar dokokin kasar Vyaccheslav Volodin ya bayyana sukar shugabansu Putin a matsayin tsokanar kasar Rasha baki daya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.