Amurka - Taliban

Taliban ta gargadi Amurka kan kin mutunta yarjejeniyar sulhu

Wasu sojojin Amurka yayin gumurzu da mayakan Taliban a saman rufin wani gida dake kauyen Dahaneh a kasar Afghanistan.
Wasu sojojin Amurka yayin gumurzu da mayakan Taliban a saman rufin wani gida dake kauyen Dahaneh a kasar Afghanistan. ASSOCIATED PRESS - Julie Jacobson

Kungiyar Taliban ta yi gargadin barkewar sabon tashin hankali a Afghanistan muddin Amurka ta ki cika alkawarin janye dakarunta daga kasar.

Talla

Mayakan na Taliban dai na raddi ne ga shugaba Joe Biden da ya bayyana shakku kan yiwuwar ficewar ta su daga Afghanistan.

Cikin makwanni 6 ya kamata Amurka ta kammala janye dukkanin dakarunta daga Afghanistan, kamar yadda yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Amurkan da kungiyar Taliban a kasar Qatar ta fayyace.

Jakadan Amurka Zalmay Khalilzad tare da wakilin kungiyar Taliban Mullah Abdul Ghani Baradar yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu a birnin Doha na kasar Qatar. 12/9/2020.
Jakadan Amurka Zalmay Khalilzad tare da wakilin kungiyar Taliban Mullah Abdul Ghani Baradar yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu a birnin Doha na kasar Qatar. 12/9/2020. AP - Hussein Sayed

A karkashin yarjejeniyar kawo karshen yakin na Afghanistan, Taliban ta yi alkawarin komawa tattaunawar sulhu da gwamnatin kasar karkashin shugaba Ashraf Ghani.

A jiya Laraba ne kuma shugaba Joe Bidan ya ce abu ne mawuyaci ya iya janye dakarun Amurka a cikin makwanni 6 da suka rage, dan haka ya soma nazari kan kalubalen, mutunta yarjejeniyar sulhun ko kuma neman karin lokaci.

Tawagar wakilan kungiyar mayakan Taliban, bayan isa dakin taron da za su sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu da Amurka.
Tawagar wakilan kungiyar mayakan Taliban, bayan isa dakin taron da za su sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu da Amurka. AP - Hussein Sayed

Sai dai yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na AFP, kakakin mayakan Taliban Zabihullah Mujahid yayi gargadin cewa ya zama dole Amurka ta janye dakarun nata kamar yadda aka cimma matsaya, idan kuma ba haka ba Amurkan ta shirya daukar alhakin dukkanin tashin hankalin da zai biyo baya.

Tuni dama Amurka ke tuhumar mayakan na Taliban da bijirewa yarjejeniyar sulhun ta hanyar cigaba da kai hare-hare a sassan Afghanistan tun bayan soma tattaunawar da suka yi a watan Satumban shekarar bara ta 2020.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.