China-Amurka

Amurka da China sun caccaki juna kan karya dokokin kasa da kasa

Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na China Xi Jinping.
Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na China Xi Jinping. REUTERS/Larry Downing

Jami'an Diflomasiyar Amurka da China sun kara da juna a tattaunawar gaba da gaba da suka yi ta farko tun bayan zuwar gwamnatin Joe Biden, yayin da kowacce kasa ke zargin yar uwar ta da aikata laifuffuka.

Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya zargi China da yi wa dokokin Duniya barazana, inda ya tabo batutuwa da dama da suka hada da halin da ake ciki a yankin Xijiang wanda ake zargin kasar da kisan kare dangi kan 'yan kabilar Uighur Musulmi da halin da ake ciki a Hong Kong da Taiwan da kutsen da ake yiwa Amurka ta intanet da tirsasawa kawayen Amurka ta bangaren kasuwanci.

Ministan harkokin wajen China Wang Yi ya zargi Amurka ta yiwa kasar sa katsalandan kan harkokin ta na cikin gida da sanyawa jami’an gwamnatin kasar takunkumi da kuma zargin kasar wajen nunawa bakaken fata wariyar jinsi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.