Amurka-Rasha

Martanin Putin kan Biden ya haifar da hatsaniya tsakanin Amurka da Rasha

Wata ganawarb Vladimir Putin da Joe Biden a shekarar 2011.
Wata ganawarb Vladimir Putin da Joe Biden a shekarar 2011. REUTERS - Alexander Natruskin

Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya yiwa takwaransa na Amurka Joe Biden shagube bayan ya bayyana shi a mtsayin mai kashe mutane, abinda ya haifar da cece kuce da kuma kiran Jakadan Rasha da ya koma gida.

Talla

Putin ya ce makashi ne kawai ke iya gane dan uwan sa, bayan ya bayyana kalaman shugaba Biden a matsayin yadda wasu jama’a ke kallon irin halayen su tare da wasu jama’a.

Sai dai shugaban na Rasha Vladimir Putin ya ce hakan ba zai sanya shi katse hulda da Amurka ba.

A larabar da ta gabata ne dai yayin zantawa da kafar yada labarai ta ABC News, Biden ya bayyana Putin a matsayin rikakken makashi 100 bisa 100, inda ya sha alwashin daukar matakin ramuwar gayya kan shugaban na Rasha.

Biden ya bayyana cewa Putin ya yi kokarin haifarwa da takararsa cikas a zaben shugabancin Amurka da ya gudana a shekarar bara ta 2020, kamar yadda binciken jami’an sirri na kasar ya tabbatar.

Sai dai da alamu martanin na Putin ya fusata Biden bayan da ya yi sammacin jakadan kasar, wanda ke tabbatar da yiwuwar sake kwabewar alaka tsakanin kasashen biyu makiyan juna.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.