Tsofuwar shugabar wuccin gadi Bolivia dake tsare na fama da rashin lafiya
Wallafawa ranar:
Tsofuwar Shugabar wuccin gadin kasar Bolivia Jeanine Ariez dake tsare,dake kuma ke fama da rashin lafiya yanzu haka ,a jiya asabar , an fice da ita daga gidan yarin da take zuwa wani gidan yari dake babban birnin kasar La Paz inda likitoci za su kula da ita.
Ana tsare da Jeanine Ariez ne bisa tuhumar ta da hannu a juyin mulkin da ya kai ga sauke tsohon Shugaban kasar Eva Morales.
An dai kama ta ranar 14 ga watan Maris tareda wasu tsofin ministoci da suka yi aiki a karkashin mulkin ta,kamu dake zuwa bayan da wata yar majalisa dake karkashin jam’iyyar tsohon Shugaban kasar ta shigar da kara a kotu.An tilastawa tsohon Shugaban kasar Eva Morales dake gudun hiira Argentina bayan gajeren lokaci a Mexico sauka daga karagar mulki a watan Nuwamba na shekara ta 2019,bayan wata kazamar zanga-zanga da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 35.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu