Australia

Mahaukaciyar ambaliyar ruwa ta kori mazauna gabashin Australia

Zuwa yanzu miliyoyin mutane aka tilastawa barin gidajensu.
Zuwa yanzu miliyoyin mutane aka tilastawa barin gidajensu. AP - Mark Baker

Rahotanni daga kasar Australia na cewa dubun-dubatan mutane na chan cikin wani hali sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya data haifar da mummunar ambaliyar ruwa, al’amarinda ya sa ake ta jigilan mutane zuwa tudin mun tsira. 

Talla

Wannan ambaliyar ruwan sama dai an dade ba’a ga irinta ba, a wannan kasa dake fama da matsalolin fari, da gobarar daji, ga kuma annobar cutar Coronavirus.

Ruwan sama da ake ta shatatawa na tsawon kwanaki, ta sagaban kogunan  New South Wales tumbatsa wadda ba’a taba ganin irinta ba na tsawon shekaru 30.

Wasu hotuna da aka dauka na yankun da aka sami ambaliyar ruwa na nuna gidaje da dama sun kusa nutsewa  ruwa,  wasu ma said ai kawai ahangi, rufin kwanonsu.

Masu aikin ceto dai na ta aikin na su a sassa daban-daban.

Ganin har yanzu ruwan sama zai cigaba, ana ganin mazauna birnin Sydney miliyan 8 da ma wasu yankunan kasar an bukaci da kowa ya zauna agida  babu batun zirga-zirga tun daga yau littini har sai anga yadda za ta kasance.

Yanzu haka dai babu wasu bayanai na rasa rayuka

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.