Ranar Ruwa

Ranar Ruwa: Mutanen karkara na shan bakar wahala

Miliyoyin mutanen karkara na shan wahala saboda karancin ruwan sha
Miliyoyin mutanen karkara na shan wahala saboda karancin ruwan sha Rodger BOSCH AFP/File

Majalisar Dinkin Duniya ta sanya ranar 22 a matsayin ranar ruwa ta duniya domin nazari kan matsalolin da al’umma musamman na karkara ke fuskanta a game da samun tsaftataccen ruwan sha da kuma lalubo hanyoyin magance su.

Talla

Taken bikin na bana shi ne mutunta ruwa fiye da farashinsa, kuma Majalisar Dinkin Duniya a bana ta ce za ta mayar da hankali ne kan gudanar da taruka domin lalubo hanyoyin inganta ruwa da kuma wadatar da shi.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren rahoto kan yadda wasu mutanen karkara a Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar suka dogara da wata rijiya daya tilo wajen samun ruwan sha

Rahoto kan yadda mutanen karkara ke dogaro da wata rijiya a Nijar

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce dole ne kasashe su tashi tsaye wajen samar da hanyoyi masu sauki da za su taimaka wa  al’ummarsu samun ruwa ba tare da wata masala ba.

Majalisar ta kuma ce za a yi gangamin wayar da kan jama’a  game da sauyin yanayi da fari da kwararowar hamada da gurbatar magudanan ruwa da rashinsa.

Tuni wasu kasashe masu tasowa kamar Nijar suka fara daukar matakin wadatar da al'ummarsu da tsaftataccen ruwan sha.

Kuna iya sauraren rahoton Rakia Arimi daga birnin Yamai.

Yadda gwamnati ke kokarin inganta hanyar samar da ruwan sha a Nijar

Game da taken bikin na bana kuwa, Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta shirya taro ta kafar bidiyo don bayyana wa al’umma muhimmancin ruwa  da kuma kauce wa barnatar da shi.

A yayin taron da za a gudanar da misalin karfe uku na yau Litinin, za a bayyana wa jama’a irin ni’imar da ke tattare da ruwa don karfafa musu gwiwar tattalin sa.

Cikin manyan bakin da aka gayyata zuwa taron har da shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis da shugaban kasar Senegal Macky Sall da Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Italiya, Jonathan Malagon Gonzales da kuma Ministan Kula da Harkokin Ruwa da Gidaje da kan Iyakoki na Colombia, Henk Ovink da sauran manyan mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.