'Yan Tawayen Yemen Sun Yi Watsi Da Tayin Sulhu Daga kasar Saudiya
Wallafawa ranar:
Kasar Saudiya ta yi tayin sasantawa da ‘yan tawayen Huthi dake Yemen, da niyyar kawo karshen yakin da ake fafatawa da su na tsawon shekaru shida. Sai dai kuma 'yan tawayen Huthi sun ce ba su amince da sulhun ba.
Wata sanarwa daga Gwamnatin Saudiya na cewa sulhun mai muhimmanci ga ilahirin kasar zai kasance karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.
Ministan waje na Saudiya Yerima Faisal bin Farhan ya fadawa taron manema labarai a Riyadh cewa butarsu itace a kawo karshen amfani da bindigogi a wannan yaki.
A yanzu haka Kungiyar ‘Yan tawayen Huthi dake Yemen sun hau kujeran naki game da wannan tayi daga kasar Saudiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu