Isra'ila-Zabe

Al'ummar Isra'ila na kada kuri'a a zaben 'yan Majalisu karo na 4 a shekaru 2

Wasu masu kada kuri'a a zaben na yau.
Wasu masu kada kuri'a a zaben na yau. REUTERS - AMIR COHEN

Yau Kasar Isra'ila ke gudanar da zaben ‘yan Majalisu karo na 4 a cikin shekaru 2 a dai dai lokacin da ake cigaba da samun rarrabuwar kawuna kan makomar Firaminista Benjamin Netanyahu.

Talla

Jami’an zaben sanye da kayayyakin bayar da kariya daga COVID-19 sun isa rumfunan zabe, tare da masu kada kuri'ar da yanzu haka ke karkashin dokar killacewa, amma kuma abin kariya da su ke sanye da shi bai wuce  kyallen rufe baki da hanci ba, sakamakon kwarin gwiwar da suka samu daga allurar rigakafin da ake yi a fadin duniya.

Firaminista Benjamin Netanyahu, mai shekaru  71, shi ne shugaban da ya fi dadewa ya na mulkin Isra’ila, kuma wanda ya fi shahara a ‘yan siyasar kasar, sai dai gazawarsa wajen kafa gwamnati mai rinjaye a majalisar dokoki ya jefa kasar cikin rikicin siyasar da ba ta taba fuskanta ba.

Kokarin kafa gwamnati bayan zabukan da aka yi a baya ya gamu da matsaloli saboda kasa samun rinjayen da Netanyahu ke bukata, abin da ya tilasta masa hada kai da abokin adawar sa Beny Gantz.

Yanzu Netanyahu na fatan masu zaben kasarsa su yi masa kara a matsayin tukuici ga kokarin da ya yi na bai wa rabin al’ummar kasar miliyan tara allurar rigakafin cutar coronavirus, da kuma nasarar da ya ci ta kulla dangataka da kasashen Larabawa da dama.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.