Isra'ila-Zabe

Netanyahu yayi ikrarin samun gagarumar nasara

Alamar kawance tsakanin Firaministan Benjamin Nethanyahu da Naftali Bennet
Alamar kawance tsakanin Firaministan Benjamin Nethanyahu da Naftali Bennet REUTERS - AMMAR AWAD

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yayi ikrarin samun gagarumar nasara a zaben kasar na 4 a cikin shekaru 2, amma rahotanni na nuna cewar zai fuskanci kalubale wajen samun kawancen da zai kafa sabuwar gwamnati.

Talla

Hasashen sakamakon zaben da manyan kafofin yada labaran Israila guda 3 suka yi, wanda ke iya sauyawa, sun nuna cewar Jam’iyyar Likud ta Netanyahu kann iya lashe kujeru mafi yawa a Majalisar dokokin kasar.

Idan hasashen ya tabbata, Jam‘iyyar Likud na iya samun kujeru 30 ko 31 a Majalisar dokokin kasar mai wakilai 120, wanda ake saran abokan kawancen sa su bashi karin kujerun da zasu iya kaiwa sama da 50 a cikin ta.

Rahotanni sun ce hanyar da Netanyahu zai bi domin samun saukin kafa gwamnati itace ta kulla kawance da tsohon abokin tafiyar sa, Naftali Bennett wanda ake hasashen cewar zai hada kai da masu adawa da Firaministan.

Netanyahu ya bayyana sakamakon zaben na jiya a matsayin gagarumar nasara ga Jam’iyyar Likud.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.