Duniya-Corona

Ana gab da samar da alluran rigakafin da za su wadaci Duniya- bincike

Kamfanoni na ci gaba da aikin samar da rigakafin na Coronavirus don wadata Duniya.
Kamfanoni na ci gaba da aikin samar da rigakafin na Coronavirus don wadata Duniya. AP - Rafiq Maqbool

Wani bincike da cibiyar DUKE mai bincke kan harkokin lafiya a Duniya da ke kasar Amurka ta fitar, ya bayyana cewa daga nan zuwa karshen shekarar da muke ciki, kamfanonin da ke samar da alluran rigakafin corona za su wadata Duniya da su. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ganin alluran da za’a iya samarwa ba za su wadaci Duniya ba.

Talla

Ta cikin rahoton binciken da cibiyar ta fitar, ta bayyana cewa zuwa karshen shekarar da mu ke ciki, kamfanonin da ke samar da alluran za su iya samar da guda biliyan 12 sama da yawan al’ummar duniya.

A cewar cibiyar wannan babban ci gaba ne kuma zai rage fargabar da ake da ita game da yaki da cutar.

Cibiyar ta kara da cewa adadin allurar da za a samar zai isa a yiwa sama da kaso 70 na yawan al’ummar duniya, idan an rabata yadda ya dace, sai dai ta koka kan yadda ake rabon allurar tsakanin kasashe masu karfin tattalin arziki da ke wawure allurar su bar matalauta da saura.

Rahoton binciken ya ci gaba da cewa matukar aka ci gaba da rabon alluran kamar yadda ake yi a yanzu, ko shakka babu duk iya yawan alluran da za a samar baza su wadaci al'ummar Duniya ba.

Rahoton ya kuma bayyana yadda kasashe masu karfin tattalin arziki za su tallafawa kamfanoni 13 da ake da su a yanzu haka masu samar da allurar, inda ya ce iyakarsu sun isa su wadatar da dukannin mutanen duniya, kuma ta haka ne za a fatattakin cutar. 

Binciken ya kara da cewa, kamata ya yi kasashen Afrika matalauta da ke karbar allurar karkashin shirin COVAX su yunkura wajen sayen ta su allurar ta kashin kansu, komai kankantar ta don hada ta da wadda ake basu ta kyauta, don kara yawan alluran da za su yiwa al’ummar su.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.