Amurka-Biden

Amurkawa miliyan 200 ya dace sun samu allurar rigakafin cutar korona

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden Jim WATSON AFP

Shugaban Amurka Joe Biden ya kaddamar da wani sabon shirin da zai kai ga ganin Amurkawa miliyan 200 sun samu allurar rigakafin cutar korona a cikin kwanaki 100 na farkon wa’adin mulkin sa, sabanin miliyan 100 da yayi alkawari a baya.

Talla

Yayin da yake ganawa da manema labarai na farko tun bayan rantsar da shi, Biden ya kuma ce tuni suka fara baiwa Amurka kudaden tallafi domin rage musu radadin rasa gurabun ayyukan yi.

Shugaban Amurka. Joe Biden
Shugaban Amurka. Joe Biden Jim WATSON AFP

Shugaban na Amurka Joe Biden gaban manema labarai ya na mai cewa

Ya zuwa jiya an sanyawa mutane sama da miliyan 100 Dala 1,400 a asusun ajiyar su, wannan kudi ne na zahiri a aljihun mutane, da zai rage musu radadi, kuma wasu karin miliyoyi zasu samu nasu nan bada dadewa ba.

A karshe tunda muka amince da shirin ceto Amurka mun fara ganin sabbin alamomin cigaba a tattalin arzikin mu, kuma yau da safe mun samu labari mutanen da suke gabatar da sunayen su saboda rasa gurabun ayyukan yi kowanne mako ya ragu da kusan 100,000. Wannan shine karo na farko a cikin shekara guda, da adadin ya fadi kafin lokacin annoba.

Har yanzu akwai sauran aiki mai karfi a gaban mu, amma abinda zan fadama Amurkawa shine, taimako yazo, kuma fata na zuwa

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.