Navalny na fuskantar azabtarwa a gidan yarin da ake tsare da shi
Wallafawa ranar:
Jagoran ‘yan adawa a Rasha Alexei Navalny, ya ce yanayin lafiyar sa na ci gaba da tabarbarewa sakamakon yadda yake fuskantar azaftarwa a inda ake tsare da shi.
Yanayin siyasar kasar ya tabarbare tun lokacin da yan sanda a kasar suka kama shugaban yan adawar kasar Akexei Navalny tare da dimbin magoya bayan sa da suka shiga wata zanga zangar adawa da shugaba Vladimir Putin da ake saran rantsar da shi sabon wa’adi na hudu a baya.
Navalny wanda ya yi kaurin suna wajen sukar lamirin shugaba Vladimir Putin, bayan komawarsa gida daga Jamus ne kotu ta yanke masa hukuncin dauri, yayin da makusantansa ke cewa yanayin lafiyarsa na ci gaba da tabarbarewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu