Alkali a Turkiya ya bukaci a daure wasu ma'aikatan Charlie Hebdo
Wallafawa ranar:
A Turkiya wani alkali mai shigar da kara a jiya juma’a ya bukaci daurin shekaru hudu ga wasu ma’aikatan Mujallar barkwanci ta Charlie Hebdo bisa tuhumar su da batanci ga Shugaban kasar Recep Tayyib Herdogan shekarar da ta gabata.
A cewar kamfanin dillancin labaren kasar Anadolu, zanen barkwonci Shugaban kasar Tayyip Erdogan an fitar da shi ne a wani lokaci da siyasar Turkiya da Faransa ya soma tsami,zanen na nuna shugaban Turkiya saye da dan karamin wando,rike da barasa a hannun sa,ya na kuma daga rigar wata mata sanye da Hijabi.
A fusace Shugaban Turkiyya ya danganta shugaban Faransa Emmanuel Macron da mara alkibila da kuma ke kiyamar addinin musulunci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu