Duniya -Sauyin yanayi

Biden ya gayyaci Buhari da shugabannin kasashe 39 taron sauyin yanayi

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. Jim WATSON AFP/Archivos

Shugaban Amurka Joe Biden ya gayyaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da wasu takwarorinsa 39 domin shiga taron matsalar sauyin yanayin da ya addabi duniya da zummar shawo kansa.

Talla

Taron na kwanaki biyu da za’a gudanar  ta kafar bidiyo zai jaddada dawowar Amurka sahun gaba wajen yaki da sauyin yanayin sabanin matsayin kasar a karkashin tsohuwar gwamnatin Donald Trump.

Fadar White House ta ce za’a gudanar da taron ne tsakanin ranakun 22 ga watan Afrilu   zuwa 23 wanda ake saran zai dada kaimi kan yunkurin kasashen duniya na shawo kan wannan matsala.

Taron zai nuna misalai kan yadda sabbin dabarun yaki da sauyin yanayi za su taimaka wajen samar da ayyukan yi masu inganci da samar da dabarun fasaha domin taimaka wa kasashen da ke fuskantar radadin sauyin yanayin.

Manyan shugabannin duniya da za su shiga taron sun hada da shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban China Xi Jinping da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Emmanuel Macron da kuma Firaministan Birtaniya Boris Johnson.

Ana saran wasu yan kasuwa da kungiyoyin fararen hula su shiga cikin taron.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.