Brazil-Coronavirus

Brazil na shirin samar da allurar Covid 19 a lokaci da cutar ke kisa a kasar

Wani mutum da ya kamu da cutar Covid 19 a Brazil
Wani mutum da ya kamu da cutar Covid 19 a Brazil AFP - MICHAEL DANTAS

Kasar Brazil na cigaba da fuskantar barrazanar cutar Covid 19,wanda cikin sa’o’I 24 aka bayyana mutuwar  mutane 3650.Yanzu haka cibiyar bincike da kuma hada maguguna ta Butantan dake Sao Paulo a kasar ta nemi izinin soma gwajin wata allurar yakar cutar covid 19 ga hukumar sa ido da kuma tabbatar da ingancin maguguna ta kasar Brazil.

Talla

A cewar masana’antar samar da wannan allura,nan da watan Yuli ,za ta iya samar da kusan  allurai milyan 40 da kuma za iya soma rarrabawa  a cikin watan.

Yanzu haka wasu rahotanni na nuni cewa kasashen Thailande da Vietnam na kera irin wannan allura .

Har yanzu Amurka ke kan gaba a tsakanin kasashen da annobar ta fi yiwa ta’adi bayan rasa akalla mutane dubu 295 da 539, sai Brazil da ta rasa mutane dubu 180 da 437, yayinda kuma a India cutar da kashe mutane dubu 142 da 628.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.