Myanmar-Amurka

Kasashen duniya sun caccaki matakin kisan masu zanga-zanga a Myanmar

Myanmar ta kasance cikin tashin hankali tun da sojoji suka karbe mulkin kasar a ranar 1 da watan Fabrairu.
Myanmar ta kasance cikin tashin hankali tun da sojoji suka karbe mulkin kasar a ranar 1 da watan Fabrairu. STR AFP/File

Ministocin tsaro na kasashe da dama sun yi tir da kisan masu zanga –zanga a Myanmar a jiya Asabar, inda akalla  mutane 90 suka mutu, cikinsu har da yara bayan da jami’an tsaro suka bude musu wuta.

Talla

 Sabuwar  gwamnatin sojin da ta kwace mulki da bakin bindiga, ta yi amfani da karfi fiye da kima a ranar da ta gudanar da bikin tunawa da sojojinta, a yayin da yawan wadanda suka mutu tun bayan juyin mulkin 1 ga watan Fabrairu ya haura akalla 423, a cewar kungiyoyi masu sanya ido a kan abin da ke gudana a kasar.

Myanmar ta kasance cikin tashin hankali tun da janar-janar din sojin kasar suka kifar da gwamnatin farar hula ta Aung San Suu Kyi, lamarin da ya jaanyo zanga-zangar neman maido da dimokaradiyya a kasar.

Ministocin tsaron kasashe 12 ciki har da na Amurka da Birtaniya, Japan da Australia sun caccaki sojin Myanmar sakamakon amfani da karfi fiye da kima a kan fararen hula.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.