Jirgin Ruwa-Suez

An janye jirgin ruwan da ya toshe hanya a mashigin Suez

An ci gaba da hada-hada bayan janye katafaren jirgin ruwan da ya tokare hanya a mashigin Suez
An ci gaba da hada-hada bayan janye katafaren jirgin ruwan da ya tokare hanya a mashigin Suez VIA REUTERS - HANDOUT

Masu aikin juya jirgin ruwan da ya makale a mashigin ruwan Masar na Suez sun yi nasarar juya shi tare da raba shi da wurin da ya tokare hanyar shigar sauran jiragen ruwa tsawon mako guda. 

Talla

Mako gudan da jirgin ya shafe a wurin ya janyo asarar fiye da Dalar Amurka biliyan tara da rabi a kowacce rana, kasancewar jiragen ruwan da ke dakon kaya daga Turai, ta nan suke wucewa.

Kamfanin Dillancin Labarai  na AFP ya ruwaito yadda aka bige da sowa da murna bayan da aka juya jirgin, kuma ya fara gangarawa a hankali kan ruwa.

An yi nasarar juya jirgin ne da misalin karfe 3 da miniti biyar naranar Litinin, kamar yadda Hukumar Kula da Mashigin Ruwan na Suez ta bayyana.

A kowacce rana, jiragen ruwa sama da 50 ne daga nahiyar Turai ke wucewa ta wannan gabar ruwan.

A jumulace, kusan kashi 12 cikin 100 na hada-hadar kasuwancin duniya na bi ta hanyar, mai tsawon kilomita 193, kuma akan shafe kusan tafiyar kilomita dubu 10 daga yankin Gulf zuwa Turai.

Kasar Faransa ce ta bude gabar ruwan a shekarar 1869, kafin daga bisani ya zama mallakin Masar a 1956

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.