Amurka-Floyd

Dan sandan da ya kashe Floyd ya ci amana-Blackwell

Marigayi George Floyd da dan sandan Amurka ya kashe bayan ya danne wuyansa fiye da tsawon minti 8.
Marigayi George Floyd da dan sandan Amurka ya kashe bayan ya danne wuyansa fiye da tsawon minti 8. AFP/Archivos

Mai gabatar da kara na Amurka ya bayyana dan sandan da ya danne wuyan  bakar fatar nan, George Floyd har lahira a matsayin wanda ya ci amanar kakinsa, yayin da shugaban kasar Joe Biden ke bibiyar shari’ar kisan da aka yi wa marigayin a bara.

Talla

Yayin da aka bude shari’ar kisan da aka yi wa Floyd, mai gabatar da karar Jerry Blackwell ya ce, dan sandan mai suna  Derek Chauvin ya saba wa dokokin aikinsa  wajen nuna rashin hankali ta hanyar  danne wuyan marigayin har sai da ya daina numfashi.

A yayin gabatar da karar, an nuna wa alkalan Minneapolis hoton bidiyo mai tsawon minti 9 da sakan 29 wanda ke nuna yadda Chauvin ya danne wuyan Floyd mai shekaru 46.

A cikin bidiyon mai tayar da hankali, alkalan sun saurari yadda Floyd ya yi ta numfasawa da kyar a daidao lokacin da masu tafiya a gefen titi suka yi dafifi suna kiran dan sandan da ya kyale bakar fatar.

Yanzu haka an tuhumi Chauvin da kisan kai, kuma yana fuskantar hukuncin daurin shekaru 40 a gidan yari muddin aka same shi da  aikata babban laifin wanda ke mataki na biyu.

Kafin fara shari’ar, lauyan iyalan Floyd da fitatun bakaken fata sun yi jawabin neman ganin an bi masa hakkinsa.

Bidiyon bakaken fata da suka yi dafifi a Amurka a yayin shari'ar.

Bakaken fata sun yi dafifi a yayin zaman shari'ar kisan da aka yi wa George Floyd

Bakaken fata sun yi dafifi a yayin zaman shari'ar kisan da aka yi wa George Floyd

Mai maagana da yawun Biden ta ce, shugaban na Amurka zai ci gaba da bibiyar wannan shari’ar kamar dai yadda Amurkawa da sauran al’ummar duniya ke sanya ido  don ganin yadda za ta kaya.

Yadda Amurkawa bakaken fata suka durkusa don karrama George Floyd da aka kashe.
Yadda Amurkawa bakaken fata suka durkusa don karrama George Floyd da aka kashe. Stephen Maturen GETTY IMAGES/AFP

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.