Ya kamata a zurfafa bincike kan kwayar Covid-19- Ghebreyesus
Wallafawa ranar:
Shugaban Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, akwai bukatar zurfafa bincike game da hasashen masana kan asalin cutar Covid-19, la’akari da rahoton da kwararru na kasa da kasa suka tattara bayan ziyarar aiki a birnin Wuhan na China.
Shugaban na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce Hukumar Lafiyar ta Duniyar ta karbi rahoton kwararrun a karshen mako, kuma har yanzu kofa a bude take domin ci gaba da nazarce-nazarce kan yadda kwayar cutar corona ta fantsama cikin bil’adama a cewarsa.
Tedros ya ce, ya fahimci haka ne bayan ya karanta rahoton kwararrun.
A cikin watannin Janairu da Fabairu ne, tagawar kwararrun na kasa da kasa ta ziyarci birnin Wuhan da ke zama makyankyasar annobar coronaviurus da zummar gano yadda kwayar cutar SARS-CoV 2 mai haddasa cutar Covid-19 ta shiga cikin jikin dan adam kafin ta fantsama a sassan duniya.
A gobe Talate ake sa ran gabatar da wannan rahoton na kwararrun a gaban kasashe 194 mambobin WHO , kafin daga bisani a wallafa shi a shafin intanet na Hukumar Lafiyar ta Duniyar.
WHO ta ce za a gabatar da rahoton Wuhan a ranar Talata
WHO says virus origins report will be released on Tuesday https://t.co/KRZQtsLtmL pic.twitter.com/y9nFpZYqT6
— Reuters World (@ReutersWorld) March 29, 2021
Rahoton na dauke da sakamakon binciken da kwararrun na kasa da kasa suka gudanar a birnin Wuhan na China.
Kwararrun za su yi cikakken bayani game da sakamakon bincikensu a Wuhan, yayin da Tedros ke cewa, yana da matukar muhimanci a kasa kunnen basira domin sauraren rahoton.
Tedros ya ce, za su tattauna da kuma nazari kan rahoton tare da fede abubuwan da ya kunsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu