WHO-Coronavirus

WHO da EU da kasashe 23 sun kulla yarjejeniyar tunkarar annoba

Taron Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.
Taron Hukumar Lafiya ta Duniya WHO. POOL/AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da kulla wata yarjejeniya tare da kungiyar kasashen Turai da kuma wasu kasashen duniya 23 domin hadin kai wajen tinkarar duk wata annobar dake iya bullowa.

Talla

Yayin ganawa da manema labarai kan shirin, shugaban hukumar Lafiya Tedros Adhanom Gebreyesus tare da shugaban Majalisar Turai sun yi Karin haske akan sabuwar yarjejeniyar da ke da nufin tunkarar bala'o'in da za su a nan gaba.

Yayin kaddamar da sabon shirin hadin kan da ya kunshi Hukumar Lafiya ta Duniya da kungiyar kasashen Turai da kuma wasu kasashen duniya 23, shugaban hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus ya ce duniya ba z ata nade hannun ta har sai an sake samun wata annobar ba.

Acewar Tedros yanzu ne lokacin daukar mataki, Duniya ba za ta sake sakaci ba har sai an kawar da wannan annoba, domin fara shirin tinkarar wata mai zuwa, yana mai cewa bai dace mu bari tunanin abinda ya faru ya bace mana ba, domin komawa yadda aka saba rayuwa ada.

Shugaban Majalisar Turai Charles Michel ya ce tabbas Duniya ta koyi darasi kan yadda aka ga annobar korona, saboda haka wannan hadin kai da zai bada damar musayar bayanai da kuma aiki tare na da matukar muhimmanci.

Shugaban na EU Charles Michel ya fara godewa Tedros da ma dukkan kasashen da suka shiga tattaunawar da aka yi domin samun cigaba, kuma har ila yau babu wanda ya tsira har sai kowa ya tsira.

A cewar Michel hakkinsu ne yin abin da ya dace, kuma abinda muke so muyi kenan wajen gabatar da wannan shawara.

Ya zuwa yanzu kasashen China da Amurka basu bayyana aniyar su ta shiga wannan kawance ba.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.