Amurka-Floyd

'Na yi nadamar rashin ceto rayuwar Floyd'

Zauren Kotun da ke sauraren bahasi a shari'ar kisan da aka yi wa George Floyd bakar fata a Amurka.
Zauren Kotun da ke sauraren bahasi a shari'ar kisan da aka yi wa George Floyd bakar fata a Amurka. AP

Matashiyar da ta dauki hotan bidiyo lokacin da dan sandan Minneapolis Derek Chauvin ya danne wuyan George Floyd har lahira,  ta bayyana nadamarta ta gaza wa wajen ceto rayuwarsa.

Talla

Darneila Frazier mai shekaru 18 na daga cikin shaidun gani da ido da suka bada bahasi a gaban kotun da ta fara shari’ar da ake yiwa tsohon jami’in 'yan sandan.

Frazier ta ce, babanta bakar fata ne, kuma tana da dan uwa bakar fata, kuma abin da ya faru ga George Floyd na iya faruwa da wani daga cikinsu.

Matashiyar ta ce, ta dauki dogon lokaci tana neman gafarar Floyd saboda yadda ta gaza ceto rayuwarsa lokacin da yake gargarar mutuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.