Majalisar Dinkin Duniya - Syria

MDD ta tara dala biliyan 6 domin tallafawa al'ummar Syria

Wasu 'yan kasar Syria da suka rasa muhallansu a sansanin 'yan gudun hijira da ke kauyen Atmeh da ke Syrian.
Wasu 'yan kasar Syria da suka rasa muhallansu a sansanin 'yan gudun hijira da ke kauyen Atmeh da ke Syrian. AP - Muhammed Muheisen

Majalisar dinkin duniya ta ce kasashe da dama sun yi alkawarin bayar da gudunmawar dala biliyan 6 da miliyan 400 domin taimakawa al’ummmar kasar Syria da yaki ya tagayyara, bayan shafe sama da shekaru 10 ana gwabza shi ba tare da ganin hasken kawo karshensa a nan kusa ba.

Talla

An dai cimma matsayar tara makudan kudaden ne a ranar Laraba, bayan kammala taron kasa da kasa kan makomar kasar ta Syria da ya gudana a karkashin jagorancin Majalisar dinkin duniya da kungiyar kasashen Turai EU.

Sai dai alkawuran gudunmawar ya gaza kaiwa adadin kudaden talllafin dala biliyan 10 da majalisar dinkin duniyar ta yi fatan samu, domin fadada taimakon da ta tsara yi zuwa kasashe masu makotaka da Syria dake karbar bakuncin dubban ‘yan kasar dake gudun hijira.

Baya ga alkawuran baiwa kasar ta Syria tallafin na dala biliyan 6 da kusan rabi, a gefe guda wasu hukumomin sun yi wa Syrian tayin ba ta bashin dala biliyan 7, domin sake gina kasar da kuma farfado da tattalin arzikinta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.