Turai-Coronavirus

WHO na zargin Turai ta kin yi wa jama'arta rigakafin Korona

WHO ta zargi Turai da jan kafa da gangan wajen yi wa jama'arta allurar rigakafin coronavirus
WHO ta zargi Turai da jan kafa da gangan wajen yi wa jama'arta allurar rigakafin coronavirus © REUTERS/Dado Ruvic/Illustration/File Photo

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta caccaki kasashen Turai dangane da jan kafar da take zargin su da yi da gangan wajen aiwatar da shirin yi wa mutane allurar rigakafin Korona. Hukumar lafiyar ta kuma bayyana damuwa kan yadda adadin masu kamuwa da cutar ke hauhawa.

Talla

Cikin sanarwar da ya fitar, Daraktan Hukumar Lafiyar ta duniya da ke kula da yankin Turai Hans Kluge ya bayyana allurar rigakafin Korona a matsayin hanya mafi saukin fita daga kangin annobar, sai dai rashin gaggauta bai wa jama’a maganin na taka rawa wajen ci gaba da kamarin cutar a sassan Turan.

Sashin Kula da yankin Turai na hukumar ta WHO ya ce, makwanni 5 da suka gabata, yawan mutanen da ke kamuwa da cutar Korona duk mako a Turai ya ragu zuwa kasa da miliyan 1, sai dai a makon da ya gabata, alkaluma sun nuna karuwar adadin masu kamuwa da cutar zuwa miliyan 1 da dubu 600 cikin mako guda a mafi akasarin kasashe 53 ciki har da Rasha da wasu kasashen yankin tsakiyar Asiya da suke mambobi a Hukumar Lafiyar ta Duniya.

Sabbin alkaluman hukumar WHO sun nuna cewar adadin mutanen da annobar Korona ta kashe a yankin na gaf da kaiwa miliyan 1, yayin da yawan wadanda suka kamu da cutar ya kusan miliyan 45.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.