Amurka

Farmaki kan ginin Capitol ya hallaka jami'in tsaron Amurka guda

Harabar ginin Capitol, Majalisar wakilan Amurka wajen da farmakin na yau ya faru.
Harabar ginin Capitol, Majalisar wakilan Amurka wajen da farmakin na yau ya faru. REUTERS - TOM BRENNER

Jami’in tsaro guda ya mutu yayinda wani guda kuma ya jikkata a wani farmaki da bai yi nasara ba kan ginin majalisar wakilan Amurka na Capitol da yammacin yau Juma’a.

Talla

Harin wanda tuni aka bindige matukin motard da ya farwa jami’an tsaron ginin da wuka a hannu, ya zo ne kasa da watanni 3 bayan yunkurin harin bom da aka gano a kan Majalisar.

Mukaddashin shugaban jami’an tsaron Majalisar Yogananda Pittman ya shaidawa manema labarai cewa matukin motar da ya nufaci kaddamar da farmakin ya yi tsalle daga cikin motar rike da hsafceceyar wuka a hannu, lamarin da ya tilastawa jami’an tsaron harbe shi nan ta ke, duk da cewa ya hallaka mutum guda tare da jikkata wani.

Har zuwa yanzu dai babu cikakken bayani game da maharin haka zalika ba a bayyana ko ya kaddamar da farmakin a radin kansa ko kuma yana wakiltar wata kungiya ta daban ba ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.