Kamfanin Pfizer da BioNTech sun tabbatar da tasirin allurar da suka samar

Allurar rigakafin cutar Covid 19 daga Pfizer
Allurar rigakafin cutar Covid 19 daga Pfizer AFP

Kamfanin Pfizer ya ce sakamakon gwajin baya bayan nan ya nuna cewar allurar rigakafin Koronar da ya samar tare da hadin gwiwar kamfanin BioNTech na da tasirin dakile sabon nau’in cutar Korona da ya soma bulla a Afrika ta Kudu.

Talla

Pfizer ya kara da cewa sakamakon gwajin a tsakanin mutane akalla dubu 46 da 307, ya nuna cewar tasirin allurar rigakafin da ya samar ya kai kashi 91.3 kan sabon nau’in cutar ta Korona.

A watan Nuwamba na shekarar 2020 ne allurar rigakafin da hadin gwiwar kamfanonin Pfizer da BioNTech suka samar, ya cimma nasarar kaiwa matakin kashi 90 na warkar da cutar coronavirus, kamar yadda kamfanonin suka sanar a baya bayan nan.

Kwakkyawan labarin nasarar gwajin allurar rigakafin ta BNT162b2 ya zo ne a daidai lokacin da aka sake samun hauhawar yawan mutanen da suka kamu da annobar ta coronavirus a sassan duniya musamman a Amurka da Turai, abinda ya tilastawa hukumomi a nahiyar sake killace miliyoyin mutane don dakile cutar da ta sake barkewa a karo na 2.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.