Mutane 49 ne suka mutu a wani hatsarin jirgin kasa a gabashin Taiwan

Wasu daga cikin masu aikin ceto bayan hatsarin jirgin kasa a Taiwan
Wasu daga cikin masu aikin ceto bayan hatsarin jirgin kasa a Taiwan VIA REUTERS - Facebook @HUALIENFASTNEWS

‘Yan sanda a Taiwan sun ce akalla mutane 49 ake fargabar sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin kasan da ya auku a gabashin yankin da safiyar yau Juma’a.

Talla

Akwai dai karin fargabar karuwar adadin mamatan, la’akari da cewar jami’ai na kan kokarin ceto wasu fasinjoji 72 da suke makale a taragan jirgin da yayi hatsarin, baya ga wasu 61 da suka jikkata.

Hukumomin yankin sun bukaci a gudanar da bincike cikin gaggawa don gano musababin aukuwar hatsarin da ya janyo asarar rayuka 49 a yankin na Taiwan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.