Amurka-Iran

Sabuwar tattaunawar Iran da Amurka na shirin ceto yarjejeniyar Nukiliyar 2015

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif.
Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif. AP - Vahid Salemi

Manyan kasashen Duniya da kasar Iran na bayyana fatar su dangane da cigaban da aka samu na shirin tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliyar Iran da Amurka ke shirin komawa ciki a taron da zai gudana makon gobe.

Talla

Kungiyar kasashen Turai ta sanar da cewar kasashen da ke cikin wannan yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2015 da suka hada da China da Faransa da Jamus da Rasha da Birtaniya sun bayyana aniyar shiga taron da za a yi ranar Talata bayan ganawar da suka yi ta bidiyo a yau.

Kasar Amurka ta ce ba za ta shiga tattaunawar kai tsaye ba tun bayan janyewar kasar da tsohon shugaban kasa Donald Trump ya yi a shekarar 2018, sai dai kungiyar Turai ta ce jami’an ta za su gana da na Amurka a kasar Austria.

Sabon shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana aniyar shiga tattaunawar muddin kasar Iran ta koma mutunta yarjejeniyar da aka kulla da ita.

Ita kuwa Iran ta ce ba za ta koma mutunta yarjejeniyar ba har sai Amurka ta janye takunkuman da ta dora mata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.