Syria - IS

Kurdawa sun kame gwamman mayakan IS a Syria

Mayakan Kurdawa a arewacin birnin Aleppo dake kasar Syria.
Mayakan Kurdawa a arewacin birnin Aleppo dake kasar Syria. © Reuters / Khalil Ashawi

Dakarun sa kai  na Kurdawa a Syria, sun bayyana kame akalla mutane 125 da suke tuhuma da zama mayakan kungiyar IS.

Talla

Kurdawan sun kame gwamman mutanen ne, bayan samamen da suka kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Hol dake arewa maso gabashin Syria.

Kakakin mayakan sa kan Kurdawa a karkashin kungiyar SDF Ali al-Hassan, ya ce zarginsu ya yi karfi ne bayan da alkaluma da suka nuna daga farkon shekarar nan zuwa yanzu an yiwa mutane akalla 47 kisan gilla a sansanin na  Al-Hol.

Kurdawan dai sun dade suna zargin cewa akwai mayakan IS dake boye a sansanin mai dauke da ‘yan gudun akalla dubu 62.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.