Nukiliya: Iran ta bukaci janye takunkuman dake kanta a lokaci guda
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce kasar ba za ta amince da matakin bi daya bayan daya ba, wajen janye takunkuman da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya kakkaba mata a shekarar 2018, domin komawa mutunta yarjejeniyar nukiliyar ta.
A baya dai Iran ta amince da shirin na bi daya bayan daya wajen janye mata takunkuman a sannu, amma ta sauya matsayinta, bayan da sabon shugaban Amurka Joe Biden ya shafe watanni ba tare fara aiwatar da matakin ba.
Yayin ganawa da manema labarai a jiya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Sa’eed Khatib-zadeh ya ce ya zama dole a cirewa kasar dukkanin takunkuman dake kanta a lokaci guda, kafin ta koma mutunta yarjejeniyar nukiliyar.
A shekarar 2018 tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, tare da lafta mata takunkuman karya tattalin arziki, bayan zargin cewar yarjejeniyar na cike da kura-kurai, matakin da ya haifar da tsamin danganta tsakanin kasashen 2.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu