Tattalin arziki- Kim Kardashian

Fitacciyar 'yar kasuwa Kim Kardashian ta zama biloniya cikin shekara 1

Fitacciyar mai shirin talabijin kuma yar kasuwa Kim Kardashian West.
Fitacciyar mai shirin talabijin kuma yar kasuwa Kim Kardashian West. Andy Kropa /Invision/AP - Andy Kropa

Mujallar Forbes dake wallafa sunayen attajiran duniya ta sanar da cewar fitacciyar mai shirin talabijin kuma yar kasuwa Kim Kardashian West ta zama biloniya shekara guda bayan kanwar ta Kylie Jennifer ta fice daga cikin jerin wadanda suka mallaki irin wadannan makudan kudade.

Talla

Arzikin Kardashian sun fito ne daga kudaden da take samu daga fitar da take a talabijin da kuma wasu kayayyakin dake dauke da sanya hannun ta.

Mujallar tace arzikin Kardashian ya tashi da sama da Dala miliyan 200 tun daga watan Oktoba bayan an kididdige cewar ta mallaki Dala miliyan 780 abinda yanzu ya zarce Dala biliyan guda.

Kim Kardashian
Kim Kardashian ASSOCIATED PRESS - Jeff Roberson

Attajiran ta kaddamar da kamfanin sarrafa kayan shafe shafe tare da yan uwan ta guda 4 da akayi ta tallata su a kafofin sada zumunta a shekarar 2017, yayin da a shekarar 2018 Forbes yace kamfanin na samun ribar kusan Dala miliyan 100.

A shekarar 2019 Kardashian mai shekaru 40 ta kaddamar da wani kamfanin sarrafa kamfe da kayan bacci da ake kira Skims wanda shi ma ya samu karbuwa a hannun jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.