Rasha-Putin

Putin zai ci gaba da zama kan karaga har 2036

Shugaban Rasha, Vladimir Putin
Shugaban Rasha, Vladimir Putin Mikhail KLIMENTYEV Sputnik/AFP/Archivos

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu  kan dokar da ke ba shi damar karin wa’adi biyu nan gaba,  lamarin da zai sa ya ci gaba da jarogancin kasar har zuwa shekarar 2036.

Talla

Shugaba Putin mai shekaru 68 wanda ya shafe fiye da shekaru 20 yana rike da madafun iko, ya rattaba hannu kan kudirin dokar kamar yadda shafin wallafa labaran gwamnatin kasar ya rawaito.

A bara ne shugaban ya gabatar da kudirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima wanda Rashawa da dama suka goyi baya a wata kuri’ar da suka kada a cikin watan Yuli, yayin da Majalisar Dokokin kasar ta amince da kudirin na shi a watan jiya.

Yanzu haka sabuwar dokar za ta sauya iyakar wa’adin shugaban kasa, abin da zai bai wa Putin damar sake tsayawa takara bayan wa’adinsa na yanzu da kuma wani wa’adin na gaba ya kare a shekarar 20124.

A shekarar 2000 aka fara zaben Putin a matsayin shugaban kasa, inda ya yi wa’adin shekaru hudu sau biyu a jere, kafin ya mika mulki ga makusancinsa Dmitry Medvedev a shekarar 2008.

A lokacin shugabancinsa, Medvedev ya sanya hannu kan dokar tsawaita wa’adin shugaban kasa zuwa shekaru shida, kuma sabuwar dokar a wancan lokaci ta fara aiki ne kan Putin bayan ya sake komawa kan karagar mulki a shekarar 2012.

‘Yan adawar kasar sun bayyana sauyin da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar a matsayin wani yunkurin tabbatar da Putin kan karagar mulki har abada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.