Amurka-Haraji

Faransa da Jamus sun goyi bayan Amurka kan harajin bai daya ga kamfanoni

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. Drew Angerer GETTY IMAGES NORTH AMERICA/AFP

Bukatar shugaban Amurka Joe Biden na sanya harajin bai daya ga manyan kamfanonin Duniya ya samu goyon bayan asusun bada lamuni na Duniya da kasashen Faransa da Jamus.

Talla

Kudirin na Joe Biden da ke shirin kawo karshen gasa tsakanin kasashe wajen sanya harajin ga manyan kamfanonin da yiwuwar ya zama babban batun da taron G20 zai mayar da hankali kansa.

Taron na G20 da zai gudana ta bidiyon Intanet a yau Laraba, zai tabo batutuwa da dama da suka kunshi hada-hadar kudi halin da annobar Covid-19 ta jefa tattalin arziki da kuma shirin tallafawa kananan kassahe da karin wa’adin biyan bashin da ke kansu, sai dai batun harajin na bai daya da ke cikin jerin manyan kudirorin shugaba Joe Biden tun gabanin hawansa mulki zai fi tattara kasashen waje guda.

Da yiwuwar dai bayan jerangiyar tattaunawa tsakanin kasashen 20 da asusun bada lamuni na Duniya da kuma bankin Duniya, a iya gabatar da kudirin tabbatar da shirin a watan Yuli.

Kafin yanzu dai kudirin na Biden na matsayin tamkar mafarki gabanin a makon jiya sakataren kudin Amurkan Janet Yallen ta sha alwashin shawo kan kasashen na G20 wajen ganin sun amince da kudirin kafin daga bisani ya samu goyon bayan kasashen Faransa, Jamus da kuma asusun bada lamuni na Duniya IMF.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.