Amurka-Floyd

An yi amfani da mugun karfi wajen kashe Floyd-Kwararre

Kisan George Floyd ya haddasa zanga-zangar adawa da cin zalin bakaken fata a Amurka da wasu kasashen duniya
Kisan George Floyd ya haddasa zanga-zangar adawa da cin zalin bakaken fata a Amurka da wasu kasashen duniya AFP/File

Wani kwararre kan aikin dan sanda ya shaida wa kotun birnin Minneapolis cewa jami’in da ake tuhuma da kashe bakar fatar nan George Floyd ya yi amfani karfi fiye da kima, abin da ya kai ga aikata kisan gillar.

Talla

Jody Stiger wanda ya kware wajen nazartar yadda jami’an tsaro ke amfani da karfi, ya yi wa kotu karin bayanin ne a yayin ci gaba da shari’a kan tuhumar Derek Chauvin, dan sanda farar fata da aka gani a hoton bidiyo ya dora gwiwarsa kan wuyan Floyd.

Stiger ya shaida wa kotu cewar, dan sanda na amfani da karfi ne sosai wajen kama mai laifi idan aka yi la’akari da irin girman laifi da aka aikata ko kuma yanayin gardamar da mai lafin ya yi a lokacin da ake kokarin kama shi.

Kwararren ya ce, babu shakka nauyin dan sanda Chauvin kan wuyan Floyd zai iya katse masa shakar iska, abin da zai kai ga rasa rai, don haka sam bai kamata dan sandan ya yi amfani da karfi ba, la’akari da yadda wanda ya kama ke kwance a kasa.

Bidiyon da ya nuna yadda Chauvin ya kama Floyd a ranar 25 ga watan Mayun 2020, ya haddasa jerin zanga-zangar dubun-dubatar mutane don nuna bacin rai kan nuna wariyar launi da cin zalin da ‘yan sanda ke yi a ciki da wajen Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.