Myanmar-London

Sojin Myanmar sun yi juyin mulkin diflomasiya a London

Hambararren ambasada Kyaw Zwar Minn ya kwana a cikin motarsa bayan an hana shi shiga cikin ofishin jakadancin Mynamar a London.
Hambararren ambasada Kyaw Zwar Minn ya kwana a cikin motarsa bayan an hana shi shiga cikin ofishin jakadancin Mynamar a London. Niklas Halle'n AFP

Birtaniya ta caccaki abin da ta kira kama-karyar da sojojin Myanmar ke yi bayan juyin mulkin diflomasiyar da suka yi wa jakadan kasar a birnin London sakamakon adawarsa da matakin kifar da gwamnatin Aung San Suu Kyi.

Talla

Jami’an diflomasiyar da ke biyayya ga sojojin Myanmar sun karbe iko da ofishin jakadancin kasar a ranar Laraba, abin da ya tilasta wa ambasada Kyaw Zwar Minn zama a waje.

Zwar Minn ya bayyana cewa, dogarin da ke tsaron ofishin ya kwace iko a wani yanayi na juyin mulki wanda ke zuwa watanni biyu da sojoji suka  hambarar da gwamnatin Suu Kyi.

Ana ci gaba da gudanar da zanga-zanga domin maido da demokuradiya a Myanmar, amma sojoji na mayar da zazzafan martanin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula  kusan 600.

A cikin watan jiya ne, sojojin na Myanmar suka yi wa ambasadan kiranye bayan ya fitar da wata sanarwa da ke bukatar sakin Suu Kyi da kuma hambararren  shugaban kasar na je ka na yi ka, Win Myint.

Ministan Harkokin Wajen Birtaniya, Dominic Raab ya nuna goyon bayansa ga hambararren ambasadan wanda ya kwana a cikin motarsa a harabar ofishin jakadancin na birnin Londan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.