Amurka-'Yan bindiga

Harin 'yan bindiga ya zama annoba a Amurka-Biden

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden © REUTERS - KEVIN LAMARQUE

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana matsalar hare-haren ‘yan bindiga dadi masu  bude wa jama’a wuta a matayin annoba, yana mai cewa ya zama dole a kawo karshenta.

Talla

Biden ya sha wannan alwashi ne yayin wani taro a fadar White House domin bayyana shirinsa na kawo karshen matsalar ta ‘yan bindiga dadi a Amurka.

Matsalar hare-haren ‘yan bindiga dadi da ke karuwa a kasar nan annoba ce, na sake fadi, matsalar ‘yan bindiga dadi a kasar nan ta zama annoba, kuma abin kunya ne a gare mu a idon duniya. inji shugaba Biden.

Shugaban ya bada misalin harin baya-bayan nan wanda ya faru a jihar South Carolina, inda wani dan bindiga dadi ya kashe wani likita da matarsa da jikokinsa 2 da hadimansa na gida.

Jim kadan da jawabin shugaban, rahotanni sun ce, an kara samun wani sabon harin bindiga da ya salwantar da rayuwar mutun guda a jihar Texas, yayin da mutane biyar suka jikkata.

Tuni aka kama maharin mai suna Larry Bollin dan shekaru 27 kuma an tuhume shi da laifin kisan kai kamar yadda rundunar 'yan sandan garin Bryan da ke gabashin Texas ta sanar.

Alkaluma sun nuna cewa, kusan mutane dubu 40 ke mutuwa a kowacce shekara a Amurka sakamakon harbin bindiga, adadin da ya ninka na masu kashe kansu da kansu a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.