Turai-'yancirani

Akalla mutane 500 ne yan Sanda suka ceto a wasu kasashen Duniya

Cibiyar hukumar yan Sanda ta kasa da kasa ta Interpol a Faransa
Cibiyar hukumar yan Sanda ta kasa da kasa ta Interpol a Faransa AP - Laurent Cirpiani

Hukumar yan Sandan kasa da kasa ta Interpol ta samu nasarar  ceto akala mutane 500 da ake bautar da su ko ake kan hanyar sayar da su ga masu fatauci don isa da su wasu kasashe daban.

Talla

Yan Sanda a wannan aiki da suka kadamar da shi tun a ranar 28 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu da kuma suka yiwa sunan Weka da yaren Swahili,manufa tsaya ta shafi kasashe 24 a Duniyar nan.

Daga cikin kasashen da yan sanda suka kai wannan samame za mu iya zana Afrika ta kudu, Kenya, Soudan JamhuriyarDemokkuradiyar Congo, Morocco, Tunisia, Spain da Girka.

A Afrika ta kudu,yan Sanda sun kama yan kasar China biyar  dake aiki karkashin wata  masaka da kuma ke amfani da ma’aikata ba bisa ka’aida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.