Iran-Amurka

Amurka na fatan cimma jituwa da Iran kan shirinta na nukiliya

Wani makami mai linzami da kasar Iran ta kera.
Wani makami mai linzami da kasar Iran ta kera. AP

Amurka  ta gabatar da wasu shawarwari ga hukumomin kasar Iran dangane da makomar yarjejeniyar nukiliyar da kasar ta cimma da manyan kasashen duniya.

Talla

Wakilan da Amurka ta aike Vienna a zaman tattaunawa da Iran na taka cancan yanzu haka duk da cewa ana sa ran kasar ta Iran za ta kawo sauyi tareda mutunta wasu daga cikin sharudodin da aka gindaya mata  a baya.

Hukumar sa ido da kuma takaita yaduawar makamai masu guba ta Duniya
Hukumar sa ido da kuma takaita yaduawar makamai masu guba ta Duniya REUTERS - LISI NIESNER

Sai dai mai magana da yahun kasar ta Iran a wannan zama Abbas Araghchi y ace babu wata tanttama daga kasar sa,fatan sa shine sauran kasashe sun  mutunta bukatun kasar ta Iran ga baki daya,hakan zai kai ga cimma matsaya ta gari tsakanin Iran da sauran kasashen Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.