Rasha-Kimiya

Dole mu ci gaba da jagorancin saman jannati-Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin a yayin jawabin cika shekaru 60 da tarihin da Yuri Gagarin ya kafa na zuwa saman jannati.
Shugaban Rasha Vladimir Putin a yayin jawabin cika shekaru 60 da tarihin da Yuri Gagarin ya kafa na zuwa saman jannati. AP - Alexei Druzhinin

Shugaba Vladimir Putin ya ce, dole ne Rasha ta ci gaba da rike matsayinta na jagora a sararin samaniya, lura da cewa, dan kasarta ne ya kafa tarihin zama mutun na farko, dan saman jannati.

Talla

Shugaba Putin ya bayyana haka ne a yayin gudanar da bikin cika shekaru 60 da Yuri Gagarin, ya yi tafiya zuwa  duniyar saman jannati a ranar 12 ga watan Afrilun 1961.

Duk da cewa a yanzu, Hukumar Sararin Samaniyar Rasha na fuskantar tarin matsaloli, amma kasar na ci gaba da alfahari saboda wannan tarihin da ta fara kafawa a duniya.

Shugaba Putin wanda ya ziyarci cibiyar da Gagarin ya sauka bayan dawowarsa daga can sararin samaniyar, ya ce, dole ne gwamnatinsa ta kara kaimi wajen tabbatar da kasar a matsayin jagora a saman jannati.

Yuri Gagarin da ya kafa tarihin zama mutun na farko da ya yi tafiya zuwa saman jannati
Yuri Gagarin da ya kafa tarihin zama mutun na farko da ya yi tafiya zuwa saman jannati AP - Alexander Zemlianichenko

A cewarsa, za su fayyace abubuwan da ake bukata domin karfafa martabarsu a wannan bangare, yana mai cewa, babu shakka batun sararin samaniya ya shafi tsaron kasa kai tsaye.

A duk lokacin da irin wannan rana ta zagayo a shekara, kafafen yada labaran kasar da suka hada da talabijin da rediyo na watsa labaran Gagarin domin tunatar da Rashawa irin gagarumar rawar da ya taka.

Ana ci gaba da tunawa da gwarzon da wata kalma da ya furta a yayin da jirginsa ke shirin tashi a wancan lokaci, inda ya ce, “Poekhali” ma’ana “zo mu je”.

Gagarin ya kafa wannan tarihin ne ya dan shekaru 27 da haihuwa, yayin da mahaifinsa ya kasance kafinta, inda mahaifiyarsa ke kiwon shanu.

Farkon dan saman jannatin ya mutu a 1968, yana da shekaru 34 a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.