Iran-Nukiliya

EU ta gargadi masu yi wa nukiliyar Iran zagon kasa

Tashar sarrafa makamashin nukilyar Iran
Tashar sarrafa makamashin nukilyar Iran AP

Kungiyar Tarayyar Turai ta gargadi duk wata kasa da ke yunkurin yi wa tattaunawar da za ta mayar da kasar Amurka cikin yarjejniyar nukiliyar Iran zagon kasa.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan da kasar Iran ta zargi Isra’ila da kai wa tashar samar da makamashin nukiliyarta  hari da ya haddasa katsewar wutar lantarki da kuma dakatar da aikin na’urori.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Kungiyar Tarayyar Turai ta ce, wannan hari da ake zargin Isra’ila da kai wa tashar nukiliyar Iran tamkar zagon kasa ne ga tattaunawar da ake yi.

Duk da babu tabbaci kan kasar da ake zargi da aikata laifin, amma dai Tarayyar Turai ta gargadi cewa, ko ma wacce kasa ce za ta dandana kudarta.

Kungiyar ta EU ta sha alwashin gudanar da bincike don gano kasar da ke da alhakin kai harin don hukunta ta, kasancewar wannan zagon kasa ne ga zaman lafiyar duniya a cewarta.

Masu sa ido dai na ci gaba da aiki tukuru don ganin tattaunawar da ake yi a birnin Vienna ta yi nasarar mayar da Amurka cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya yi fatali da ita.

Tuni shugaban Amurka Joe Biden ya ce, a shirye yake ya mayar da Amurka cikin yarjejeniyar don dawo da kyakyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da ta yi tsami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.