Ramadan

Saudiya ta tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan

Saudiya ta sanar da gobe Talata a matsayin 1 ga watan Ramadan
Saudiya ta sanar da gobe Talata a matsayin 1 ga watan Ramadan REUTERS/Iqro Rinaldi

Hukumomin Saudiya sun sanar da ganin jinjirin watan Ramadan, abin da ke nufin cewa, gobe Talata za a fara azumin Ramadan.

Talla

Jaridar Saudi Gazette da ake wallafawa a Saudiya ta rawaito daga Kotun Kolin Kasar cewa, gobe Talata na a matsayin 1 ga watan Ramadan, shekara ta 1442 da hijirar Manzan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

Kotun Kolin ta ce,  an gudanar da zama na musamman domin karbar shaidar mutanen da suka ce, sun hangi jinjirin watan a wannan yammaci a kasar.

Bayan karbar shaidar, kotun ta kuma tabbatar da ganin watan a yankuna da dama  da suka hada da tsakiyar kasar ta saudiya.

A karo na biyu kenan da Musulman duniya za su gudanar da ibadar azumin Ramadan cikin annobar Covid-19 wadda ta lakume rayukan miliyoyin mutane a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.