Amurka - Zanga-Zanga

Zanga-zangar adawa da zaluncin 'yan sanda ta sake barkewa a Amurka

Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da cin zalin 'yan sanda a garin Brooklyn Center dake birnin Minneapolis a kasar Amurka.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da cin zalin 'yan sanda a garin Brooklyn Center dake birnin Minneapolis a kasar Amurka. © AFP/Kerem Yucel

Zanga-zanga ta barke a birnin Minneapolis na kasar Amurka bayan da wani dan sanda ya bindige wani bakar fata har lahira.

Talla

Lamarin na zuwa a daidai lokacin da ake shari’ar dan sandan da ake tuhuma da halaka wani bakar fata George Floyd a dai birnin na Minneapolis.

Jim kadan bayan aukuwar lamarin a daren jiya Lahadi, daruruwan mutane ne suka yi dandazo a gaban ginin babban ofishin ‘yan sandan garin Brooklyn Center dake birnin Minneapolis a jihar Minnesota, lamarin da ya tilastawa jami’an tsaro harbawa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa.

Wani daga cikin masu zanga-zanga yayin kalubalantar 'yan sanda a garin Brooklyn Center dake birnin Minneapolis a Amurka.
Wani daga cikin masu zanga-zanga yayin kalubalantar 'yan sanda a garin Brooklyn Center dake birnin Minneapolis a Amurka. © Photo by Christian Monterrosa via AP

Kate Wright, mahaifiyar Daunte Wright matashin bakar fatar mai shekaru 20 ta shaidawa taron jama’a cewar, dan nata ya kira ta a waya inda ya shaida mata cewar ‘yan sanda sun tsayar da shi a motarsa, kuma ta ji lokacin da suke shaida masa ya yanke kiran wayar da yayi, daga bisani kuma daya daga cikin ‘yan sandan ya kwace tare da kashe wayar.

Kate Wright ta kara da cewar jim kadan bayan aukuwar hakan ne budurwar dan nata ta shaida mata cewar an harbe shi, yayin da fasinjar dake tare da Daunte Wright ta jikkata.

Cikin sanarwar da ta fitar rundunar ‘yan sandan garin Brooklyn Center dake Minneapolis ta ce jami’anta sun tsayar da matashin da ya rasa ransa ne saboda karya dokar tukin da yayi, bayan gajeren bincike ne kuma suka yi yunkurin tsare shi, bayan gano wasu laifukan na karya dokokin tukin dake kansa, amma sai yayi musu gardama inda ya koma cikin motarsa, abinda ya sanya daya daga cikin ‘yan sandan dake wurin dirka masa harsashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.