Afghanistan-Amurka

Amurka ta kammala cimma manufofin da suka kai ta Afghanistan

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. AP - Andrew Harnik

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewar kasar ta cika manufofin da suka kai ta kasar Afghanistan kuma zai janye dakarun sa zuwa gida daga ranar 11 ga watan Satumba mai zuwa.

Talla

Yayin da ya ke jawabi na musamman kan shirin janye sojojin, Biden ya ce ya dace a duba zaman sojojin Amurka a Afghanistan kan dalilin da ya kai su kasar na ganin sun hana amfani da Afghanistan wajen kai wa kasar su hari.

Shugaban ya ce a matsayin sa na shugaban Amurka na 4 da ya jagoranci yakin Afghanistan lokaci ya yi da dakarun su za su koma gida, amma za su janye su ne cikin tsari kuma a tsanake.

Biden ya ce za su dauki matakin ne tare da tintibar kawayen su na kasashen Duniya.

Ita ma kungiyar tsaro ta NATO ta sanar da cewar za ta fara janye dakarun ta daga Afghanistan daga ranar 1 ga watan Mayu mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.