Amurka-Afghanistan

Amurka za ta janye sojinta baki daya daga Afghanistan

Yau shugaba Joe Biden zai fayyace yadda zai janye dakarun Amurka baki daya daga Afghanistan.
Yau shugaba Joe Biden zai fayyace yadda zai janye dakarun Amurka baki daya daga Afghanistan. REUTERS - KEVIN LAMARQUE

A yau Laraba shugaban Amurka Joe Biden ke gabatar da jawabin fayyace yadda gwamnatinsa za ta janye daukacin dakarun kasar daga Afghanistan.

Talla

Hukumomin Amurka sun ce, ana sa ran janye dakarun gabanin cika shekaru 20 da kaddamar da harin ranar 11 ga watan Satumba, abin da zai kawo karshen yakin da kasar ta shiga mafi tsawo da abokan gaba a tarihinta.

A can baya, shugaba Biden ya yi ta nazari game da yiwuwar rage wani adadi na dakarun a Afghanistan domin ragargazar mayakan al-Qaeda ko kuma mayakan ISIS.

Sai dai a yanzu, shugaban ya sauya shawara, inda zai janye dakarun na Amurka baki daya.

Daukar matakin janye dakarun daga Afghanistan na zuwa ne duk da cewa, ana ci gaba da dari-dari kan hare-haren da mayakan Taliban ke kaddamarwa a kasar.

Kazalila daukar matakin na Biden na zuwa ne bayan Turkiya ta sanar da shirya taron kasa da kasa da zai tattauna kan samar da zaman  lafiya mai dorewa a Afghanistan  wadda ta shafe kusan shekaru 40 tana fama da yaki.

Sai dai mayakan Taliban sun ce, za su kaurace wa wannan taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI