Iran-Nukiliya

Iran za ta kaucewa tattaunawa marar amfani kan Nukiliyarta- Khamenei

Shugaban addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei.
Shugaban addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei. AFP - -

Shugaban addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yi gargadin kaucewa doguwar tattaunawa tsakanin kasar da manyan kasashen Duniya dangane da shirin nukiliyarta wanda ya ce zai iya yiwa Tehran illa.

Talla

Yayin da ya ke tsokaci ta kafar talabijin, Khamenei ya ce su na taka tsan tsan wajen tattaunawar da manyan kasashen duniya ta hanyar da ba zai taimakawa Iran ba, dai dai lokacin da ake shirin komawa kan teburin tattaunawa gobe Alhamis a Vienna.

Kasashen yammacin Duniya sun sake bayyana aniyar su ta ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran, yayinda kasar ta bukaci cire mata takunkuman da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya mayar mata kafin mutunta ka'idojin yarjejeniyar ta 2015.

Tun a makon jiya ne aka faro tattaunawar bayan aniyar Joe Biden na Amurka da ke fatan gyatta yarjejeniyar ta 2015 don hana Iran mallakar makamin Nukiliya, inda a bangare guda kasar ke sanar da shirin kara yawan makamashin uranium din da ta ke tacewa zuwa kashi 60 wanda ke gab da adadin da ake bukata ga karfin Soji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.